Kungiyan masu maganin gargajiya sun sharwarci shugaba Buhari ya nemi maganin asibiti

Kungiyan masu maganin gargajiya sun sharwarci shugaba Buhari ya nemi maganin asibiti

- Kungiyar masu maganin gargajiya sun nuna gamsuwar su da yadda shugaba Buhari ke yaki da rashawa da kuma Boko Haram

- Kungiyar sun ce a shirya suke su taimaka ma shugaba Buhari da magani idan ya bukaci hakan

- Shugaban kungiyar Cif Oluwawo yace matsalolin rayurwamu suna da nasaba da watsi da al’addun mu na gargajiya da mukayi

Kungiyar masu magungunan gargajiya mai suna ‘Aegis Association of African Traditional Religions and Medicine Practioners’ wanda aka fi sani da Iseese Agbaye sun baiwa shugaba Buhari shawara da ya cigaba da amfani da maganin asibiti domin neman waraka daga rashin lafiyar sa.

Masu magananin gargajiyan sun nuna gamsuwar su da yadda shugaba Muhammadu Buhari yake kokarin magance cin hanci da rashawa da kuma kawar da yan Boko haram.

Kungiyan masu maganin gargajiya sun sharwarci shugaba Buhari ya nemi maganin asibiti
Kungiyan masu maganin gargajiya sun sharwarci shugaba Buhari ya nemi maganin asibiti

Sun kuma ce a shirye suke su taimaka ma shugaban wajen samun lafiya a duk lokacin da ya bukace su.

DUBA WANNAN: Sanata Na'Allah ya karkatar da kwangilar rijiyan burtsatsai zuwa gidansa

Shugaban kungiyan, Cif Awoyemi Abinbola Oluwawo ya shaida wa manema labarai jiya a garin Erin-lle cewa, “Muna fuskantan matsaloli da yawa a rayurwa mu da kuma kasar mu saboda munyi watsi da al’addun mu na gargajiya, zamu iya samar da maganin da zai warkar da shugaba Buhari a nan gida Najeriya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164