Asibitin koyarwa na Shika ya kama hanyar sukurkucewa

Asibitin koyarwa na Shika ya kama hanyar sukurkucewa

- Asibitin ABUTH ya zama abin da ya zama a yanzu

- Wani bincike ya nuna yadda asibitin ya sukurkuce

- Jama'a da dama dai sun mutu a dalilin sakaci da gangaci

Asibitin koyarwa na Jamia'ar Ahmadu Bello da ke Garin Shika ya kama hanyar sukurkucewa a halin yanzu.

Asibitin koyarwa na Shika ya kama hanyar sukurkucewa
Yadda asibitin ABUTH ke kashe marasa lafiya

Wani bincike na musamman da aka gudanar a sashen fida na mata da maza da sashen yara da na karbar haihuwa da na kula da mata a asibitin koyarwar na Jamia'ar Ahmadu Bello da ke Shika ya nuna yadda ganganci da sakacin Jami'ai yake sanadiyar mutuwar marasa lafiya.

Asibitin koyarwa na Shika ya kama hanyar sukurkucewa
Kazanta raga-raga a Asibitin Shika

Tashin farko dai masu bara ne su ka cika bakin shiga asibitin da rokon banza. Haka kuma cikin asibitin yayi raga-raga musamman yankin kula da yara da karbar haihuwa. Wani abu ma sai ka leka cikin ban dakin asibitin wanda daga nesa za ka ji wari da zarni na kadowa. Saboda irin wannan kazanta ne har ta kai ana daukar wata cuta a asibitin wajen neman lafiya. Kai akwai Likitan asibitin da yace mani an taba daukar dogon lokaci ba a yin fida saboda rashin ruwa ko na wanke hannu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi magana ga Najeriya

Asibitin koyarwa na Shika ya kama hanyar sukurkucewa
Bangaren Asibitin koyarwa na Shika

Daga cikin irin abubuwan da ke kai ga mutuwar Jama'a akwai:

Malaman asibitin kan yi shirme wajen daukar bayanin maganin maras lafiya. Akwai wadanda su ka ce irin wannan yayi sanadiyar rashin 'Yan uwan su yayin da aka sayo magani a waje aka ajiye ba ayi amfani da shi ba har aka rasa mai ciwo.

KU KARANTA: An ba Dan Najeriya damarDigiri kyauta

Bayan nan kuma su ma Likitoci kan canzawa mutum magunguna dabam-dabam kamar yadda ake canza su lokacin aiki. Akwai wanda ta kashe sama da N63,000 wajen sayen magani irin wancan da wancan lokacin da yaron ta yake fama da cutar kuna kwanan nan.

Bayan nan kuma akwai sakaci da rashin kula daga Likitocin wanda hakan kan saa karamar matsala ta zama babba. Sai a dauki lokaci ba ayi aiki ba ana jiran a samu wuta ko kayan aiki daga kasuwa. Da dama sun rasa rai a dalilin wannan a asibitin.

Asibitin koyarwa na Shika ya kama hanyar sukurkucewa
Kayan datti a Asibitin Shika

Bari dama dai da dama daga cikin manyan Likitocin su na da asibiti na kan su inda su ke aika maras lafiya da an ji wata-wata. Kai abin ya kai marasa lafiya na tserewa zuwa wasu asibitocin na Gwamnati kuma su samu sauki.

Yanzu haka dai duk wanda ya san asibitin ya san ya kama hanyar jagwalgwalewa. Da dama kuma su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tsadar kaya ya kawo matsala a Jihar Osun

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng