YANZU-YANZU: Baba Buhari ya dira da karfi (hotuna)
Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya dawo daga birnin Landan misalign karfe 5 na yamma yau Asabar, 19 ga watan Agusta, 2017 bayan ya kwashe kwanaki 100 da yan kai yana jinya a Landan.
Shugaba Buhari ya dawo ne tare da dogarinsa da wasu masu kula da shi a birnin Landan. Manyan jami’ab gwamnati wanda ya kunshi ministoci, yan siyasa, ne suka tarbesa a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja.
Da safiyar yau mun samu rahoton cewa shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau Asabar, 19 ga watan Agusta.
KU KARANTA: An yi ram da wani fasto kan laifin algush
Mun samu wannan rahoto ne daga bakin mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ta shafin ra’ayi da sada zumuntarsa na Facebook inda yace:
“ Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo yau bayan ganawa da likita a Landan. Shugaban kasan ya bar kasa ranan 7 ga watan Mayu ne bayan mike ragamar mulki ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, wani ya zauna a matsayin mukaddashin shugaban kasa.
Ana sa ran shugaba Buhari zai yi magana da yan Najeriya misalign karfe 7 na safe ranan Litinin, 21 ga watan Agusta,2017."
Ya mika godiyarsa ga yan Najeriya wadanda suka sanya shi cikin addu’a tun lokacin da Allah ya jarabesa.
Don bamu shawari ko labari, aiko mana sako 'labaranhausa@corp.legit.ng'
https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/
https://www.twitter.com/naijcomhausa/
Asali: Legit.ng