Mun kagara shugaba Buhari ya dawo gida - inji Sheikh Sani Yahaya Jingir
Shahararren malamin islaman nan a Najeriya watau Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir wanda kuma shine shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'ikamatus Sunnah watau Izala a takaice ya bayyana cewa suna murna da farin cikidangane da yadda shugaba Muhammadu Buhari yake kara murmurewa.
Shahararren malamin ya kuma cigaba da bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi da sauran ministocin sa suna da kishin Nijeriya a ransu don kuwa sun taimaka matuka wajen dawo da martabar Najeriya a idon duniya.
Legit.ng ta samu daga majiyar mu cewa Sheikh Jingir ya yi wannan bayyanin ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sa a jiya Juma'a a wani masallacin 'yan Taya dake cikin garin Jos a arewa ta tsakiyar Najeriya.
Daga karshe Sheikh Jingir ya ja hankalin wadanda shugaba Buhari ya baiwa mukamai da su ji tsoron Allah. Ya kuma yi wa shugaba Buhari addu'ar Allah ya kara masa lafiya.
Asali: Legit.ng