Maiduguri: Gwamna Shettima ya yi wasu sabbin nadi 24
- Gwamna Shettima ya nada wasu sababbi masu ba da shawara 24 a jihar
- Ciki har da wasu tsofoffin mataimakin gwamnan jihar su biyu
- Shettima ya amince da nada wasu sakatariyar dindindin da shugabanin kananan hukumomin na wucen gadi
Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya amince da nada karin masu ba da shawara 24. Sun hada da mashawarcin musamman 17 da masu shawarar musamman guda 7.
Ciki har da tsofoffin mataimakin gwamnan jihar su biyu, Alhaji Adamu Shettima Yuguda Dibal da Alhaji Ali Abubakar Jatau sun kasance daga cikin masu ba da shawara.
Sauran sune Farfesa Emeritus Umaru Shehu, Engr. Ibrahim M. Ali, Farfesa Dili Dogo, Barr. Bashir Maidugu da kuma Alhaji Idrisa Timta.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Jidda Shuwa, a cikin wata sanarwa inda aka ba da jerin sunayen masu ba da shawara kamar su Misis Zara Bukar, babban mashawarci game da harkar zuba jari da Adamu Kachalla, ciniki da zuba jari da Nuhu Clark, ma'aikatar RRR da kuma Samson Dibal, gidaje da makamashi.
KU KARANTA: Famanen Sakatare da ake zargi da satar dukiyar kasa ya dawo da biliyoyi ga gwamnati
Sunday Madu Gadzama,harkar Ilimi da Cif Kester Moghalu, dangantakar al’umma da Engr. Lawan Abba Wakilbe, SUBEB da Abba Nguru, Ilimi mafi girma da Dokta Toma Rangiya, harkokin addini da Engr. Muhammad Wakil Dongo, muhalli da kuma Hajjiya Zuwaira Gambo, harkokin mata.
Sauran su ne Daniel Musa Malang, ofishin mataimakin gwamna da Tukur Mshelia, labarai da al'adu da Hussaini Gambo, binciken ƙasa da Umar Abdullahi Jara Dali, tarwatarda talauci da Zarma Mustpha, ayyuka da sufuri da kuma Da Al-Bashir Ibrahim Saleh, BOSIEC.
Shettima ya kuma amince da nada wasu sakatariyar dindindin da shugabanin kananan hukumomin na wucen gadi a jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng