Murnan cika shekaru 76: tarihin Najeriya ba zai cika ba har sai an ambaci sunan IBB – Inji Saraki

Murnan cika shekaru 76: tarihin Najeriya ba zai cika ba har sai an ambaci sunan IBB – Inji Saraki

- Tsohon shugaban kasa a mulkin Soja ya cika shekaru 76

- IBB ne shugaban kasa na 9 a jerin shuwagabannin Najeriya

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin wani muhimmin ginshiki ne a siyasar Najeriya.

Jaridar The Nation ta ruwaito Saraki na fadin haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, a lokacin dayake taya tsohon shugaban kasar murnan cika shekaru 76 a rayuwa.

KU KARANTA: An kama baƙin haure ɗan ƙasar India da wani Inayamiri suna siyar da jabun magani a kasuwannin Kano (Hotuna)

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun Saraki Yusuph Olaniyonu yana bayyana IBB a matsayin daya daga cikin iyayen kasa masu fada a ji, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban kasar nan.

Murnan cika shekaru 76: tarihin Najeriya ba zai cika ba har sai an ambaci sunan IBB – Inji Saraki
IBB da Saraki

“Ire iren shawarwarin da IBB ke bayawar a kasar da kuma tsokaci daya saba yi lokaci zuwa lokaci sun taimaka wajen ciyar da kasar nan gaba.

Murnan cika shekaru 76: tarihin Najeriya ba zai cika ba har sai an ambaci sunan IBB – Inji Saraki
IBB da Saraki

“Ina mai fatan alheri da kuma tsawon rai tare da karin shekaru masu albarka. Da fatan Allah ya albarkaci rayuwarsa, ya tsare shi, kuma ya kare shi. Amin.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wani abinci kafi kauna, kalla:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng