Gaskiyar zance: Shin masu fafutukar kafa kasar Biafara sun mallaki makamin Nukiliya?

Gaskiyar zance: Shin masu fafutukar kafa kasar Biafara sun mallaki makamin Nukiliya?

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin ma'abota kafar sadarwar nan ta zamu watau 'social media' a turance watakila sun ci karo da wani labarin da ke nuna wani hoton makami mai linzami da aka ce wai wani dan kabilar Ibo ne ya kera wa masu fafutukar ganin an kafa kasar Biafra.

To binciken da gidan jaridar nan namu mai farin jini da ingantattu kuma sahihan labari na Legit.ng ya gudanar ya gano cewa labarin dai na kanzon kurege ne watau dai bai inganta ba.

Binciken namu ya gano cewa gidan jaridar nan ne na Vanguard ya fara buga labarin a daren jiya inda suka bayyana cewa wai wani ne dan kabilar Ibo mazaunin kasar Rasha ne da ya dawo gida ya kera shi kuma ya sa masa suna Biafra Satan 404.

Gaskiyar zance: Shin masu fafutukar kafa kasar Biafara sun mallaki makamin Nukiliya?
Gaskiyar zance: Shin masu fafutukar kafa kasar Biafara sun mallaki makamin Nukiliya?

To sai dai binciken namu ya nuna mana cewa gidan jaridar ya nuna matukar rashin kwarewa a harkar aikin jarida domin kawai ya samu makaranta labarin nasa ta hanyar yaudarar su da labarin na karya musannan yanzu da hankulan mutane da yawa suka raja'a kan maganar ta Biafra.

Binciken namu dai har ila yau ya bankado cewa wanda ma ya rubuta labarin mai iya rubuta sunan kasar ta Rasha da turanci dai-dai ba inda ya rubuta 'Rusia' a maimakon 'Russia'.

Gaskiyar zance: Shin masu fafutukar kafa kasar Biafara sun mallaki makamin Nukiliya?
Gaskiyar zance: Shin masu fafutukar kafa kasar Biafara sun mallaki makamin Nukiliya?

Haka ma dai wani binciken da mukayi kamar yadda wani ma'abocin kafar sadarwar Gimba Kakanda ya fallasa wani shafin gidan jarida na HUFFPOST shine ya fara wallafa hoton a shafin sa kimanin shekaru 5 da suka shude a ranar 19 ga watan Yuni na shekarar 2013.

Asali: Legit.ng

Online view pixel