Jerin Kasashen da saki ya zama ruwan dare
- Mun kawo maku jerin kasashen da su ka fi saki a aure
- Abin mamaki Najeriya ba ta shiga cikin na farko ba
- A wasu kasashen ma a kan raba Dukiya idan an rabu
Yau kuma mun kawo maku jerin kasashen da su ka fi sakin aure ne a fadin Duniya. Kasashen dai mafi hawa da su kayi fice na Turai ne kamar yadda masu nazari su ka fada. Abin mamaki Najeriya ba ta shiga cikin sahun farko ba alhali akwai mutuwar aure sosai a Kasar.
1. Kasar Belgium
2. Kasar Portugal
3. Kasar Hungary
4. Kasar Czech
5. Kasar Spain
KU KARANTA: An kama wani da kan mace a Legas
6. Kasar Luxemburg
7. Kasar Estonia
8. Kasar Cuba
9. Kasar France
10. Kasar USA
Kasar Amurka ce dai ta 10 wajen rabuwar aure. A Duniya kaf a wannan lokaci babu irin kasar Belgium inda a shekara a kowane minti guda a kan samu mutane kusan 10 da za su sheka Kotu domin a raba auren su. A irin wannan kasashen dai a kan raba Dukiya bayan an raba auren.
An kalato wannan daga Worldtopposts
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Me mata ke nema wajen maza?
Asali: Legit.ng