Luwadi da dalibi mai shekaru 4 – An damke wani Hedmasta

Luwadi da dalibi mai shekaru 4 – An damke wani Hedmasta

Yadda masifa ta sauka akan wani hedi mastan makaranta domin ya zakkewa wani dalibi mai shekaru 4

Wani hedi-mastan makaranta Sule Yusuf, ya gurfana a gidan kaso bisa zargin shi da laifin aikata luwadi da wani dalibi.

Sule, mai shekaru 57 a duniya, ya aikata wannan laifin ne a ofishin sa na makaranatar Salihawa Firamare dake karamar hukumar Musawa a jihar Katsina.

A cewar rahoton farko da ofishin ‘yan sanda ya samu, ya bayyanawa kotun majistire ta Katsina cewa, mai garin Tungen Zuri, Kabiru Hussaini ne ya shigar da kara ofishin na ‘yan sanda dake wajen gari.

Luwadi da dalibi mai shekaru 4 – An damke wani Hedi-masta
Luwadi da dalibi mai shekaru 4 – An damke wani Hedi-masta

Ya bayyanawa ‘yan sanda cewa, mahaifiyar wannan dalibi wadda mazauniyar kauyen Gidan Ranau ce, ta kawo ma sa cewa Mallam Sule ya aikata lalata da dan ta.

Jami’in dan sanda, Sani Ado, mai shigar da karar a gaban kotu ya ce, wannan laifi ya sabawa sashe na 284 na final kot kuma har yanzu bincike ya na nan bai kare ba.

KU KARANTA: Ketare iyaka yana haifar da rikicin manoma da makiyaya – Tambuwal

Ita kuwa mai shari’ar wannan kara, Fadila Dikko, ta daga sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Agusta kuma ta bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a gidan Kaso har zuwa lokaci na gaba.

Ta kuma jaddadawa Mallam Sule cewar, kotun ta ba ta damar tambayar sa akan ko ya aikata wannan laifi ko sabanin haka sai dai babbar kotu ce ta ke da damar zartar da hukuncin wannan laifin da ake tuhumar shi da shi.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: