Tsohon Shugaban Kasar Amurka Barrack Obama ya bar tarihi
- Tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama ya bar tarihi
- Barrack Obama ya kafa wani tarihi a Duniyar yanar gizo
- Wani hoto da Shugaban ya dora a shafin sa ya samu karbuwa
Ko ku na da labari cewa Tsohon Shugaban kasar Amurka watau Barrack Obama ya bar tarihi a kafafen yada labarai na zamani.
Shugaba Obama ya kafa wani tarihi a Duniya inda wani hoto da ya dora a shafin sa na Tuwita ya samu karbuwa wajen Jama'a a Duniya. Kusan akalla mutane Miliyan 2 da rabi wannan hoto ya burge a shafin sadarwa na Tuwita. Wannan hoton ne na 3 wurin farin jini a Duniya.
KU KARANTA: Gargadi mai gina ramin mugunta
A hoton dai an ga Barrack Obama tare da wasu kananan yara kusa da shi inda ya rubuta cewa babu wanda ake haifa da kiyayyar wani. Obama na kokarin nunawa Duniya dai cewa su so juna ba kamar yadda wasu ke kokarin kawo rashin soyayya a tsakani ba.
Kwanaki kun ji cewa bayan shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya sauka daga mulki bai wuce ko ina ba sai gidan haya. Haka ma Mataimakin sa Joe Biden wanda ya fi shekaru 29 a Majalisar Dattawa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko Harry Song ya kai gwarzo?
Asali: Legit.ng