Yan Najeriya na ta cece-kuce akan ziyarar da Sanusi Barkindo ya kai wa Buhari a birnin Landan
- Hotuna sun nuna Barkindo da yayan sa suna shan hannu da Buhari
- Gidan Abuja ya zama gidan Tarihi da kowa da kowa ke kai zaiyara
- Buhari ya zama shugaban kasan Hoto
Yan Najeriya suna ta cece-kuce akan hotunan ziyarar da sekataren kungiyan OPEC Sanusi Barkindo ya kai wa Buhari a gidan Abuja dake birnin Landan.
A ranar Litinin mai taimaka wa shugabankasa ta harkan watsa labarai, Garba Shehu ya fitar da hotunan a shafinsa na tuwita.
Hotuna sun sa cece-kuce a shafin ‘yada zumunta na facebook a tsakanin yan Najeriya.
Wasu sunce gidan Abuja dake birnin Ladan yazama Kaman gidan tarihi da kowa ke halarta, wasu kuma sunce Buhari yazama shugabankasan hoto.
KU KARANTA: Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida
Ebipade Emiyaibo: “Idan na samu kudi zan dauki iyali na da abokai na zuwa gidan tarihi Landan dan ganin Buhari.”
Biafara Uche: “Sakarkaru ne kadai suka yarda da cewa Buhari na raye, in ba haka yayi magana da birrai yan uwansa ta shafin Skype”
Friday Nekabiri Edoo: “Shugaban kasar hoto”
Breakthrouh Uchenna: “Shirme kawai. Wa ya damu da shi?"
Ikong Christian: “A wannan zamanin babu abun da ba zai iya faruwa ba ta yanar gizo."
Gerald chukwu: “Allah ya baka lafiya. Muna kewan ka sosai kuma muna jiran dawowar ka.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng