Wasu kalmomin da Turawa su ka aro daga Yaren Najeriya
- Akwai wasu kalmomin da Turawa su ka aro daga Najeriya
- Turawa sun ari wasu kalmomi daga Ibo da Hausa da su Ibibio
- Daga cikin wadannan kalmomi dai akwai irin su Juju da sauran su
Kamar kwanakin baya wannan karo mun kawo maku jerin wasu kalmomi da aka aro daga harsunan Najeriya zuwa Ingilishi.
Kadan daga ciki:
1. Okra
Asali wannan kalma daga harshen Ibo aka dauko ta. Turawa na kiran kubewa da Okra a harshen Ingilishi.
2. Bogus
Asali wannan kalma daga Hausa ta fito kamar yadda masana su ka fada. Yanzu Bature kan yi amfani da wannan kalma.
KU KARANTA: Ayyukan da ke gaban Shugaba Buhari
3. Juju
Asali ma dai Juju kalmar daga Najeriya aka dauko ta. Juju na nufin abin da ya shafi Aljanu ko kuma wata rawa ta mutanen mu.
4. Tango
Haka dai kalmar Tango asali daga harshen Ibibio na mutanen Kasar Kudu ta fito wanda ainihi rawa ne na mutanen Yankin.
5. Buckra
A yaren mutanen Efik, Buckra na nufin Bawa wanda Turawa su ka ara su ke kiran bakin mutum ko kuma Talaka farin fata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Rikici tsakanin Yan siyasar kasar
Asali: Legit.ng