A kul! Kada ka kuskura ka ci bashi don yin waɗannan abubuwa guda 3

A kul! Kada ka kuskura ka ci bashi don yin waɗannan abubuwa guda 3

jaridar Daily Trust tayi nazari inda ta fitar da wasu abubuwa guda uku da bai dace mutum ya karbi bashi ba domin gudanar dasu, ko ya tafiyar dasu. Wadannan abubuwa sun hada da:

1- Kada kaci bashi don biyan Albashi

A matsayin mutum na dan kasuwa, ya dace ka guji karbar bashin banki kona wasu wai don ka biya kudin albashin ma’aikatan ka alawus dinsu. Idan hart a kai ga kudin ka ba zai iya biyan albashinsu ba, toh ka rage ma’aikata.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Buhari ya tarbi sakataren ƙungiyar man fetur da Duniya a Landan (Hotuna)

Ma’ana a sallami ma’aikatan da basu da wani muhimmin amfani, sai a bar masu himma daga cikinsu, wadanda kudin da kasuwancin naka ke samarwa zai iya biyan su albashi.

A kul! Kada ka kuskura ka ci bashi don yin waɗannan abubuwa guda 3
Bashin kudi

2- Guji siyan kayan gwari da kudin bashi

Bai kamata dan kasuwa ya ciyo bashi don ya sayo kayan gwari ba, abin nufi kayayyakin da ba zasu dade ba, ba tare da sun lalace ba, musamman a wannan yanayin da jama’a basu da kudin kashewa.

Kaga kenan da zarar jama’a basa iya siyan kayan ka, toh fa lallai sai dai ko ka siyar da arha kayi asara, ko kuma kayan naka su lalace. Don haka ake shawartar yan kasuwa da su ciyo bashi akan kayan da zasu dade basu lalace ba.

Abu na Uku da majiyar Legit.ng ta yi ma yan kasuwa kashedi akansa shine:

3- Kada ka ciyo bashi don siyan mota ko gidan zama

Abinda yafi dacewa da dan kasuwa mai dabara shine ya dage wajen tsimi da tanadi, musamman a halin karayar tattalin arziki, don haka kada ka mutum ya ciyo bashin da zai iya durkusard a kasuwancinsa.

Musamman cin bashi don siyan ababen jin dadi, wadanda ba zasu kara ma kasuwancin ka komai ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wasu gyara za'ayi a Najeriya?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng