Kalmomin Larabci da aka aro a harshen Hausa

Kalmomin Larabci da aka aro a harshen Hausa

- Hausawa sun ari wasu kalmomi daga harshen Larabci

- Daga cikin irin wannan kalmomi akwai sukari da Aljani

- Ko me ya hada Malam Bahaushe haka da Balarabe?

Ba shakka Malam Bahaushe ya ari wasu kalmomin sa daga harshen Larabci. Da yawa dai daga ji za ka fahimci daga inda aka kalo su. Ga dai wasu 5 nan daga ciki yau da mu ka kawo:

Kalmomin Larabci da aka aro a harshen Hausa
Hausawa a wajen wani biki

1. Sukari

Da Larabci ana cewa As-sukar wanda kuma shi ne Bature ya ke kira Sugar. Ko daga wajen wa aka fara aro kalmar?

2. Kofi

Bature ma dai ya kan kira Kofi da suna CUP watau abin da Balarabe yake kira KAUB. Ka kuma dai ji wani sabo!

3. Al-Jinn

Shi Bahaushe kamar Balarabe ya san da Aljannu abin da Larabawa ke kira Al-jinn. Turawa ma dai yanzu su kan kira su Jinns da Ingilishi.

KU KARANTA: Samarin Katsina za su fatattaki Inyamurai

4. Albasa

Kusan a yare da dama Albasa ba ta canza suna ba a Najeriya. Haka dama aka san wannan suna wajen Balarabe watau Al-baslun.

5. Sabulu

Sabulu ma dai da Larabci asalin sunan sa Sabun. Bayan wadannan dai akwai aron kalmomi da dama tsakanin Hausa sa Larabci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko me mata ke bukata wajen maza?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng