Allah ya karbi ran wata maniyyaciya a filin tashin jirgin sama a Sokoto

Allah ya karbi ran wata maniyyaciya a filin tashin jirgin sama a Sokoto

- In ajali yayi kira ko babu ciwo dole a tafi Inji masu iya magana

- Allah yayi wa wata maniyyaciya aikin hajjin bana rasuwa kafin su tashi

- An samo sunanta da Inno Mu'azu daga jihar Kwara

Allah ya nauki ran wata maniyyaciya yar asalin jihar Sokoto mai suna Inno Mu’azu, ta rasu ne a filin tashin jirgi na Sultan Abubakar III da ke Sokoto.

Inno, mai shekaru 56 a duniya ta rasu ne a yayinda take kokarin shiga jirgin a ranan Alhamis da yamma.

Allah ya karbi ran wani maniyaci a filin tashin jirgin sama a Sokoto
Allah ya karbi ran wani maniyaci a filin tashin jirgin sama a Sokoto

Jami’in hulda da jama’a na hukumar alhazai na jihar Sokoto, Alhaji Faruk Umar ya tabbatar da rasuwan nata a ranar Juma’a.

Shima mai Magana da yawun Maniyyatan jihar Sokoto, Alhaji Isa Shuni ya tabbatar da labarin rasuwar, yace Inno Mu’azu yar asalin karamar hukumar Kware ne kuma bata da wani rashin lafiya tare da ita.

DUBI WANNAN: Maiduguri ta dau dimi bayan soji sunyi wa ofishin majalisar duniya kawanya

A cewarsa, anyi mata duk gwaje-gwajen da ya kamata kuma ba’a same ta da wani rashin lafiya ba amma sai ta kawai ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take kokarin shiga jirgin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yayanta maza guda biyu suma sun yanke jiki sun fadi bayan rasuwar nata, amma dai daya daga cikinsu ya farfado a filin tashin jirgin, shi kuma dayan yana asibiti yana karban magani.

Shugaban tawagar maniyyatan jihar kuma babban Alkalin jihar Sokoton, Mai shari'ah Bello Abbas ya mika sakon ta’aziyan sag a iyalenta kuma yayi addua’a Allah ya gafarta mata kuma ya saka mata da Aljanna Firdausi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: