Aminin Shekarau, kuma Tsohon shuagaban jam’iyyar ANPP ta jihar Kano ya rasu
A ranar Laraba 10 ga watan Agusta ne Allah yayi ma tsohon shugaban jam’iyyar ANPP, Alhaji Sani Hashim Hotoro rasuwa, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Marigayi Hashim ya rasu ne a babban Asibitin koyar na Malam Aminu Kano dake jihar Kano, bayan yayi fama da rashin lafiya sakamakon cutar suga data addabe shi.
KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda
Alhaji Hashim ya rasu ya bar mata biyu, yaya 14 da jikoki da dama, kuma tuni aka yi jana’izarsa a gidansa dake kusa da masallacin juma’a a Hotoro, kamar yadda yaronsa, Saidu Hashim Hotoro ya bayyana ma majiyar Legit.ng.
Hashim Hotoro ya taba zama shugaban jam’iyyar ANPP har na tsawon shekaru takwas din da gwamna Malam Ibrahim Shekaru ya kwashe yana mulkin jihar Kano.
Jama’a da dama sun halarci jana’izarsa, cikinsu har da shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, da kuma tsohon kwamishina Alhaji Rabiu Dansharu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng