Dandalin Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda

Dandalin Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda

- Masarautar Bidda ta karrama dan wasan Hausa Sani Danja

- Sarkin Bidda Alhaji Yahaya Abubakar ya nada Danja Zakin Arewa

Shahararren jarumin Kannywood Sani Danja ya samu mukamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda dake jihar Neja a ranar Asabar 5 ga watan Agustan bana, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mai martaba Sarkin Bidda Alhaji Yahaya Abubakar ne ya nada Sani Danja sarautar gargajiyan, inda ya nada shi sarautar Zakin Arewa, inji majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Rundunar Sojin sama ta zazzaga ma mayaƙan Boko Haram ruwan bama bamai (Bidiyo)

Daruruwan masoya fitaccen jarumin sun yi dafifi a wajen bikin nadin sarautar daya wakana a fadar Sarkin Bidda, inda aka jiyo wata masoyiyarsa, Aisha Yusufu tana fadin nadin sarautar tasa yazo a daidai lokacin daya dace.

Dandalin Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda
Sani Danja

“Sani Danja tauraro ne a Kannywood, kuma yana taimaka ma matasa da dama suna cin ma burinsu a fannoni daban daban.” inji Aisha Yusufu.

Dandalin Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda
Sani Danja

Mawaki Sani Danja, kuma mai yin shirin wasan kwaikwayo ya samu daukaka a harkar fim da wake wake sakamakon irin rawar dayake takawa, da kuma irin shigar da yake yi.

Ga bidiyon nadin sarautar nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Menene babban bukatar mata daga maza, kalla:

Asali: Legit.ng

Online view pixel