‘Yan Majalisan Arewa da dama ba su tabuka komai
- ‘Yan Majalisan Arewa da dama albashi kurum su ke karba kurum
- Da dama dai ba su da kudiri ko guda tun hawan su zuwa yanzu
- A Jihar Kano akwai ‘Yan Majalisa da dama a wannan sahun
Da yawan ‘Yan Majalisar kasar nan sai tara kudi kurum su ke yi ba tare da wani aiki ba. Ciki har irin su Alhassan Ado Doguwa ba su da kudiri ko guda.
Mafi yawan ‘Yan Majalisar Arewa dai ba su gabatar da kudirin komai ba musamman na Yankin Arewa maso yamma. Asali cikin su 91 ta kai har mutane 60 ba su gabatar da kudiri ko daya ba. Jaridar Daily Trust tayi wannan nazari.
KU KARANTA: Nawa ne albashin 'Yan Majalisa?
A Arewa maso gabas ma dai fiye da rabin ‘Yan Majalisar cikin su 48 ba su yi komai ba. A Arewa ta tsakiya kuwa ‘Yan Majalisa 16 ne kurum ba su da wani kudiri da sunan su. Daya daga cikin su shine Dan Majalisar Birnin Tarayya.
A Jihar Kano Alhassan Ado Doguwa da su Honarabul Ibrahim Sani Umar, Abdullahi Mohammed Gaya, Garba Umar Durbunde, Nasiru Baballe Ila, Suleiman Aliyu Romo, Sani Mohammed Rano, Munir Babba Dan-Agundi, Nasiru Ali Ahmed, Shehu Usman Aliyu, Musa Ado Tsamiya, Mustapha Bala Dawaki da Badamasi Ayuba ba su da kudiri ko daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi yadda wani saurayi yake hada kudi da gumin sa
Asali: Legit.ng