Ko ka san nawa 'Yan Majalisa su ka samu daga hawan zuwa kawo yanzu?
- 'Yan Majalisa sun karbi albashin sama da Miliyan 200
- A kowane wata dai su kan tashi da Naira Miliyan 10
- 'Yan Majalisar kasar dai sun ci fiye da rabin wa'adin su
Kamar yadda ku ka ji 'Yan Majalisar Najeriya sun karbi albashin sama da Miliyan 200 cikin shekaru biyu.
Lissafi ya nuna cewa kusan watanni 20 ne dai kacal su ka ragewa 'Yan Majalisar kasar su sauka daga mulki. Kowane Dan Majalisar ya samu kudin aiki na kusan Naira Miliyan 8 sannan kuma ga wasu 'yan kari na kusan Miliyan guda.
KU KARANTA: Ba abin da wasu 'Yan Majalisa su ke yi
Tun da a wata kowane na tashi da sama da Miliyan 8 kenan cikin fiye da shekaru biyu kowa ya karbi akalla Naira Miliyan 214. An dai kashe fiye da Naira Biliyan 32 wajen albashin 'Yan Majalisan Kasar daga 2015 zuwa yanzu.
Jaridar Daily Trust tayi wannan nazari inda tace dai kusan kusan rabin 'Yan Majalisa ne su ka gabatar da kudiri tun hawan su Gwamnati yayin da sauran 'Yan Majalisa fiye da 160 kenan dai ba su gabatar da wani kudiri ba kamar yadda ku ka ji.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kaji yadda wani Saurayin ke tara na sa kudin!
Asali: Legit.ng