Maiduguri: Gwamnatin Borno ta kashe naira biliyan 14 a kan gina hanyoyi 22

Maiduguri: Gwamnatin Borno ta kashe naira biliyan 14 a kan gina hanyoyi 22

- Gwamnatin jihar Borno ta ce ta kashe naira biliyan 14 ga ayyukan gine gine hanyoyin a fadin jihar

- Lawan ya ce an gina hanyoyin tsakanin 2016 da 2017 a wasu sassan jihar

- Gwamnatin jihar ta kuma samar da motocin sufuri 32 ga kamfanin sufurin na jihar

Gwamnatin jihar Borno ta ce ta kashe akalla naira biliyan 14 akan gina hanyoyi 22 a cikin shekaru biyu da suka wuce.

Alhaji Adamu Lawan, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Lawan ya ce an gina hanyoyin ne tsakanin 2016 da 2017 a wasu sassan jihar.

Maiduguri: Gwamnan Borno ya ce naira biliyan 14 a kan gina hanyoyin 22
Gwamnan jihar Borno, Kashin shattima

Ya ce an kammala ayyukan 26 daga cikin ayyukan 60, a na ci gaba da wasu 13, yayin da 22 kuma na jiran amincewa.

KU KARANTA: Boko Haram sun rusa gidaje miliyan daya, ajujuwa makaranta 5000, dukiyan kimanin N1.9 trillion a jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno

Lawan ya ce ayyukan da aka kammala sun hada da Bulumkutu-Tsallake da Abbaganaram-Gongolong da Magoram da Bulabulin da kuma Legas street.

Sauran su ne Mala Kachalla-Ibrahim Taiwo Housing, Airport da Ndurimari, inda ya kara da cewa ayyukan sun hada da gina wani gada a Legas street da kuma magudanar ruwa da dama.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta kuma samar da motocin sufuri 32 ga kamfanin sufurin na jihar Borno Express Transport Corporation don inganta aikinta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel