Sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranci kafa majalisar koli ta malamai na darikar Tijjaniyya a Najeriya
Shehu Usman Dahiru Bauchi ya yi jagora ga manyan yan darikar Tijjaniya wadanda suka hada da Shehunai, Khalifofi, Muqaddamai da sauran mabiya darikar baki daya.
An dauki kwanaki biyu ana gudanar da taron a garin Bauchi, wato a ranakun Jumaá da Asabar.
Manyan Shehunnai, Khalifofi da Mukaddamai sun halarci wannan gagarumin taro da mabiya darika suka shirya.
Anyi kira ga mabiya Darika da su kaunaci junansu, su so junansu, su dunga ziyartar juna, sannan kuma suyi biyayya ga juna, kuma kowa ya amince cewa daga yanzu za’a dinga magana da murya bai daya ne.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki na ma shugaba Buhari adduán dwowa lafiya – Shehu Sani
Kuma wadanda suka samu halarta su sanarwa wadanda ba su zo ba. Daga karshe, takardar sakamakon taro za’a rarraba shi ga dukkan Zawiyyoyi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng