Yanzu na gane gaskiya: Dalilai 3 da su ka sa na bar Shi'a-Hussain Brother
- Wani Kasurgumin Dan Shi'a a baya ya tsere ya bar ta
- Yace yanzu ya gane gaskiya bisa ikon Allaah
- Tsohon Dan Shi'an yace ya daina zagin Sahabbai
Mun samu labari daga wani mai suna Salihu Babban Tanko cewa wani rikakken Dan Shi'a a baya mai suna Hussein Ahmad Malumfashi ya tsere ya bar ta inda yace ya gane gaskiya.
Daga cikin dalilan sa na dawowa Ahlus-Sunna dai akwai:
1. Ali RA ya goyi bayan Abubakar RA
Imam Ali da kan sa yayi wa Sayyidina Abubakar mubaya'a ya mara masa baya kenan babu sabani ko zargin zalunci a tattare da su.
2. Ali RA ya aurar wa Umar RA
Duk da irin abin da ake fada tsakanin su, ta tabbata cewa Sayyidina Aliyu RA ya dauki Diyar sa ta ciki ya ba Sayyidina Umar RA aure wanda ke nuna karya ake yi da ake cewa akwai gaba.
3. Sunayen 'Ya 'yan Ali RA
Bayan aure kuma har ta kai Sayyidina Ali RA ya rika radawa 'Ya'yan sa sunayen su Abubakar da Umar dsr
Hussein Ahmad Malumfashi da aka fi sani sa Brother ya fi shekaru 30 yana Addinin Shi'a yace yanzu ba takiyya bace ya tuba!
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Abubuwan da ke cikin matsala a Najeriya
Asali: Legit.ng