Labarin wata mata da sha guba saboda mijinta ya mare ta a fuska
Wani mutum ya yi danyen hukunci da ya dadawa matar sa mari saboda ta yiwa dan su hukuncin wani laifi da ya yi mata inda ita kuma ta sha maganin kashe kwari ko ta huta da fushi
An samu rahoto daga mazauna kauyen Eruemukohwarien na karamar hukumar Arewacin Ughelli da ke jihar Delta cewa wata mata ta sha maganin kashe kwari saboda mijinta ya mare ta wai don ta daki dan su bisa wani laifi da ya yi ma ta.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wannan mata, Stella Oghenerohwo mai shekaru 33 da haihuwa, ta sha maganin kashe kwari kuma ta rinka dabawa cikinta kaifi saboda mijinta, Prince Sylvester Oghenerohwo ya mare ta a fuska bayan ta daki dan su bisa wani laifi da ya yi wanda ba a bayyana ba.
Kakakin 'yan sanda na jihar Delta, DSP Andrew Aniamaka wanda ya tabbatar da faruwar wannan abu ya ce, "An kawo mu su rahoton ne ofishin su na Ughelli da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Asabar.
"An kawo mana rahoton cewa, mijin wannan mata, Prince Sylvester Oghenerohwo ya dadawa matar ta sa mari saboda ta daki dan su sanadiyar wani aike da ta yi ma sa, wanda wannan mari ya fusata wannan mata ta sha maganin kashe kwari kuma ta yi amfani da fasashiyar kwalba ta rinka dabawa cikinta yanka"
KU KARANTA: Mulkin Najeriya: Fayose zai bayyana ra'ayin sa na tsayawa takara
"Ba bu wani tabbaci da ya ke nuna ko za a gurfanar da wannan mata a kan laifin na yunkurin kashe kanta."
Kuma ta na asibiti wanda ba a bayyana sunan shi ba inda ta ke karbar kulawa kuma an cigaba da bincikar wannan al'amari," a cewar Andrew.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng