Zandoro: an gano mutumin da yafi kowanne ɗan Najeriya tsayi (Hotuna)
- An bayyana wani bawan Allah a matsayin mutumin da yafi kowa tsayi a Najeriya
- tsayin wannan mutumi ya kai kafa 7 da inchi 4
Ikon Allah sai kallo, jaridar Legit.ng ta yi karo da wani mutumi wanda tsananin tsawo, wanda har hakan ta kai ga ana ganin babu wani mahaluki a Najeriya kaf daya kai shi tsawo.
Wannan matashi mai suna Hafiz, an kara masa da inkiya Agoro (wanda ke nufin tsawo a yaren yarbanci) saboda tsananin tsayinsa, da hakan ta tabbatar lallai shine wanda yafi kowa tsawo.
KU KARANTA: Ma’aikatan kamfanin Dangote sun yi masa satan naira miliyan 451
Sai dai a kwanakin baya ma Legit.ng ta ruwaito labarin wani matashi mai suna Bakare Olalekan, wanda tsawon say a kai kafa 6 da inchi 8, amma idan ka hada shi da Hafiz, Hafiz ya fi shi.
Shafin yanar gizo na Wikipedia ta bayyana cewa akwai sama da mutane 100 wanda tsayinsu ya haura kafa 7 a duniya, don haka a’a iya sassautawa ace wata kila a samu wadanda suka fi Hafiz din tsayi a Najeriya.
Amma tunda ba’a gano su ba zuwa yanzu, a iya cewa Hafiz Agoro ne yafi kowa tsayi a Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli irin halittar wata mata:
Asali: Legit.ng