Bahaushe mai ban haushi: Kazamin rikici ya barke tsakanin al'ummar Hausawa 2 a Legas
Labaran da muke samu da dumi dumin su na nuni da cewa yanzu haka dai wani kazamin rikici ya barke a jihar Legas a babbar kasuwar nan ta safarar kayayyaki ta Alabarago a tsakinin bangarori biyu na jama'ar Hausawa mazauna yankin.
Yanzu haka ma dai wasu rahotannin daga jihar na cewa an ruga da mutune takwas zuwa asibiti wadanda aka ji wa rauni a lokacin bata kashin.
Legit.ng ta samu labarin cewa musababbin rikicin dai baya rasa nasaba da kokarin da ake yi na a sasanta tsakanin wasu bangarori biyu da ke zaune a kasuwar da basa jituwa da juna a kan shugabancin na kasuwar.
Haka ma dai majiyar ta bi ta ayyana cewa tuni dai har mahukunta a jihar sun tura jami'an tsaro na 'yan sanda zuwa yankin. Haka zalika kuma har yanzu 'yan sanda ba su ce komai ba kan batun.
Asali: Legit.ng