Tir! Wata waka da aka fitar cikin yaren Hausa ta ci ma kabilar Ibo mutunci
- Kabilun Najeriya sun dade suna kyamatar juna babu gaira babu sababi
- An sha jin irin wadannan kalaman batanci daga bangarorin kabilun Najeriya
- A lokuta da dama ana samun asarar rayuka yayin da kalaman kin juna suka yi yawa
Wata waka da wasu samari da 'yan mata suka rera da yaren Hausa na nan ta cika gari, wadda kuma take cike da muggan kalamai na batanci da cin zarafin wasu al'ummu da ke zaune tare da mu.
A irin wannan kalamai a baya ma, Legit.ng ta rahoto muku yadda wani saurayi ke kira da a tashi a kashe jama'a a kona dukiyarsu, wanda ya zuwa yanzu dai ba'a kamo shi ba, balle ya fuskanci hushin hukuma.
Suma na kudun suna kan zaafa kalaman batanci ga sauran al'ummu dake zaune dasu wadanda ba 'yan asalin yankin ba. Inda sukan yi kira da a kona Najeriya ko ma mutanensu su zo su balle domin kafa tasu kasar.
Yakin basasar da ya faru a lokutan baya dai a 1967-70 yayi ma Najeriya asarar rayuka fin miliyan daya, sannan ya tsayar da yankin kudun maso gabas ci gaban shekaru.
Ya zuwa yanzu dai wasu masu kiran kansu samarin arewa da su ma na kudun suna ta kara yada kalaman kin juna a tsakanin al'umma, abin haushin kuma shine, wai kamar da yawun kowa suke magana, wanda hakan ba haka yake ba, domin kabilun da ke zaune lafiya da juna sun fi masu neman rigima da yawa.
DUBA WANNAN: Wa'adin kamo Shekau na kwana 40, shin me sojin suka taka ne?
Fatan mu dai, shuwagabanni da talakawa na wannan zamani, su dena koyi da iyayen Najeriya na farko, wadanda suka koya mana tsana da kabilanci, addinanci da bangaranci, wadannan shuwagabanni dai sune har yau muke gani a manyan kasa, kuma su muka saka a kan kudadenmu na Naira da muke amfani da ita, daga kowanne bangare na kasar nan suka fito kuma.
Wakar dai ta muzanta kabilar ta Ibo, cikin kalamai da ba wanda zai so a gaya masa, ta kuma kira su da 'yan ashi, barayi, wai kuma ma wai su suke shigar burtu suyi ta'addanci a yankin arewa maso gabas ace wai Boko Haram ce.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng