Bauchi: An yi jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi (Hotuna)

Bauchi: An yi jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi (Hotuna)

- An yi jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi a Azare

- Jana’izar ta samu halartar gwamnan jihar tare da wasu jami’in gwamnati

- Gwamnan ya bayyana mutuwar a matsayin asara ga duk 'yan siyasa da al'umma baki daya

An yi jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, marigayi Alh. Muhammad Garba Gadi a bisa ga addinin Musulunci a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta a garinsa Azare da ke jihar Bauchi.

Mai martaba gwamnan jihar Bauchi, Mohammed A. Abubakar ya halarci Jann’izar tare da jami’in gwamnatin jihar ciki har da babban shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Arch. Audu Sule Katagum.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, gwamna Mohammed A. Abubakar ya bayyana marigayin Gadi a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana da kuma amintacce. Gwamnan ya kuma bayyana mutuwar a matsayin asara ga duk 'yan siyasa da al'umma baki daya.

Bauchi: An yi jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi (Hotuna)
Jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, marigayi Alh. Muhammad Garba Gadi

Jana’iza ta kuma samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar, RT. Hon. Kawuwa Shehu Damina da mai martaba sarkin Misau da kuma mai martaba Alh. Ahmed Sulaiman da sauransu.

KU KARANTA: EFCC: Tsohon gwamnan Adamawa ya kalubalanci EFCC ta kai shi kotun koli

Allah ya ji kansa da rahama ya kuma sa Aljanat Firdaus ne makomarsa, ya kuma kyautata na mu karshe. Amin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel