Keffi: Al-makura ya gabatar da sandan sarauta ga sabon sarkin Kefi
- An nada sabon sarkin keffi, mai martaba Dr. Shehu Chindo Yamusa 111
- Gwamna Tanko Al-Makura ya gabatar da sandan sarauta ga sabon sarkin a ranar Asabar
- Wasu mazunar garin Keffi sun yaba kokarin gwamna Almakura wajen nada sabon sarkin domin ya gaji mahaifinsa
Gwamna Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa, a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta ya gabatar da sandan sarauta ga sabon sarkin Keffi, Dr. Shehu Chindo Yamusa 111.
Legit.ng ta ruwaito cewa sabon ya gaji a mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Chindo Yamusa 11, wanda Allah yai wa rasuwa a watan disamba 4, 2015. Tsohon sarkin na da shekaru 70.
Daruruwan al’ummar jihar sun fito domin halarcin taron bikin bayar da sandan wanda ke da halartar gwamnoni da ministoci da 'yan siyasa da sarakunan gargajiya da kuma sauran mutane.
Wani mazaunar garin Keffi, wanda ya yi magana a kan sabon sarkin, ya bayyana shi a matsayin wani dattijo na gari cewa zai taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar.
KU KARANTA: Aikin hajji: Saudiyya ta yi karin kudi ga wadan za su je a karo na 3 ko fiye na N240,000
Mista Ali Garba, daya daga cikin mazaunar garin, ya bayyana cewa sabon sarkin mutum ne mai son zaman lafiya da kuma hadin kai al’ummarsa.
Mista James Godwin, wani mazaunin, ya yaba wa kokarin gwamna Almakura wajen nada sabon sarkin domin ya gaji mahaifinsa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng