Masu sana'ar karuwanci 72 sun shiga hannu a jihar Benuwe

Masu sana'ar karuwanci 72 sun shiga hannu a jihar Benuwe

Wata kungiyar mata ta yi zanga-zanga a jihar Benuwe don bayyana kukan ta akan al'amarin yawaitar yiwa kananan yara fyade a jihar wanda sanaiyar haka ne gwamnatin ta cafke ma su sana'ar karuwanci har 72 a jihar.

A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Benuwe tare da hadin gwiwar 'yan sandan jihar suka kai simame gidajen karuwai 5 wanda su ka cafke kimanin guda 72 a birnin Makurdi.

Wannan kamen na karuwai ya bayu ne sanadiyar da wata kungiyar mata su ka nuna kukan su da yin zanga-zanga a kan yadda yiwa kananan yara fyade da lalata su yake karuwa a jihar.

Shugaban mai baiwa gwamntin jihar shawara a kan harkokin tsaro, Col, Edwin Jando ya bayyanawa wannan kungiyar ta mata cewa gwamnatin gwamna Samuel Ortom ba za ta lamunci wannan gurbatanci da yake faruwa a jihar ba.

Masu sana'ar karuwanci 72 sun shiga hannu a jihar Benuwe
Masu sana'ar karuwanci 72 sun shiga hannu a jihar Benuwe

Jando ya ce yunkurin da gwamnatin jihar ta ke wajen kawar da faruwar fitintinu a jihar ne ya sa suka cafke wannan karuwai a gidajen sana'ar su.

KU KARANTA: Hanyoyin kauce wa ambaliyar ruwa a Najeriya

Shugabar kungiyar ta mata ma su zanga-zanga, Magdalene Gbazua ta ce, kungiyar ta su ta yi wannan abu ne saboda an samu faruwar fyade da lalata kananan yara guda 15 wanda suke tsakanin shekaru 2 zuwa 7 na haihuwa a jihar kuma babu abinda ya faru ga wadanda suka aikata wannan laifi.

Gbazua ta ce lalacin da a ka yiwa 'yar shekaru 14 ta jihar Legas wanda sanadiyar haka ne ta rasa ranta ya assasa wannan zanga-zanga, kuma ta na gargadin gwamnatin jihar Benuwe da ta tabbatar da kwakkwaran mataki a kana ma su aikata wannan laifi kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayar da dama tun shekarar 2015.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel