‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi kowa albashi
- Dan wasa Carlos Tevez na kan gaba wajen albashi
- Har yanzu Neymar bai doke Dan wasan da ke China ba
- A kowace rana ta Allah Neymar na da Naira Miliyan 30
Jaridar Daily Mail ta kawo jerin ‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi kowa albashi a Duniya tun bayan da Neymar Jr. ya bar Barcelona zuwa kungiyar PSG.
Dan wasa Carlos Tevez na kan gaba wajen albashi. Har yanzu Neymar bai doke Dan wasan na Argentina da ke taka leda a Kasar China ba. Duk Turai dai babu mai samun kudi yanzu haka irin Dan wasa Neymar.
KU KARANTA: Sana'ar da ta fi kawo kudi a Duniya
Bayan nan akwai manyan ‘Yan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo da Gareth Bale da kuma irin su Lionel Messi na Barcelona.
- Carlos Tevez
- Neymar
- Ezequiel Lavezzi
- Oscar
- Lionel Messi
- Cristiano Ronaldo
- Gareth Bale
- Hulk
- Gervinho
- Axel Witsel
Ko barci Neymar yayi ya tashi a rana ba mamaki zuwa wannan lokaci ya hada kusan Naira Miliyan 10 a sabon Kulob din da ya koma PSG.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kudi za su saye soyayya?
Asali: Legit.ng