Badaƙalar gidan N700,000,000: Sheikh Gumi ya caccaki mai alfarma Sarkin Musulmi

Badaƙalar gidan N700,000,000: Sheikh Gumi ya caccaki mai alfarma Sarkin Musulmi

- Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya soki lamirin siyan ma Sultan gidan N700m

- Shehin Malamin yace irin wannan son duniyar ke jefa mu cikin bala'i

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana kaduwarsa gami da bacin rai dangane da labarin da ake watsawa na cewa za’a siyan ma mai alfarma sarkin Musulmi gidan naira miliyan 700.

Gumi ya bayyana damuwarsa a shafin Facebook, inda yace: “Yunwar mu na jin dadin duniya ne ke kashe mu, yake hallakar da miliyoyin yan kasar mu, ace duk da matsalar rashin biyan albashin ma’aikata, rashin aikin yi, amma za’a siyan ma wani gidan hutawa na naira miliyan 700.

KU KARANTA: Yaƙi da almundahana: Kotu ta yanke ma ma’aikacin gwamnati macuci zaman gidan yari shekara 1

“Ire iren wannan abubuwan ne ke sanya matasan mu gogoriyin zaman shuwagabannin, kuma hakan ne ke jefa matasan mu zuwa ga rungumar ta’addanci.” Inji Gumi.

Badaƙalar gidan N700,000,000: Sheikh Gumi ya caccaki mai alfarma Sarkin Musulmi
Sheikh Gumi

Legit.ng ta ruwaito Gumi yana fadin “Naso in yi shiru kamar yadda na saba yi a baya tun lokacin dana fahimci tsananin munafuncin dake damun mu yan Najeriya. Allah yace “Yak u wandanda kuka yi imani, meyasa kuke fadin ba kwa aikatawa? Ya kai laifi a wajen Allah ku dinga fadin abinda ba kwa aikatawa. Q 61/2-3.”

Gumi ya kara da fadin rashin adalcin shugabannin ne ya janyo mana bala’o’i daban daban da muke fama dasu a kasar nan.

Badaƙalar gidan N700,000,000: Sheikh Gumi ya caccaki mai alfarma Sarkin Musulmi
Gidan da za'a siyan ma Sarkin Musulmi

Daga karshe Gumi yace, shi yana ganin kamata yayi a dinga yaki da ta’addanci a boye da kuma gaskiya tare a bada muhimmanci ga yafiya da neman hadin kan kasa don samun nasarar yakin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kamata yayi a shafe shuwagabannin Najeriya daga doron kasa, kalla:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng