Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara

Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara

- Yanzu Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara

- A kowace rana ta Allah zai tashi da sama da Naira Miliyan 30

- A kowace awa guda Dan wasan zai samu sama da Miliyan guda

Ko barci Neymar yayi ya tashi a rana ba mamaki zuwa wannan lokaci ya hada kusan Naira Miliyan 10 a sabon Kulob din da ya koma PSG.

Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara
Sabon Dan wasan PSG Neymar

Dan wasan da a cikin talauci ya tashi ya amince da yarjejeniyar shekaru biyar inda za a kashe kudi har sama da Dala Miliyan 500. A kowace rana ta Allah Neymar zai tashi da akalla Naira Miliyan 36.

KU KARANTA: Hira da Baturiyar 'Yar wasa

Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara
Dan wasa Neymar ya koma Faransa

Da mu kayi lissafi dai mun fahimci cewa Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin sama da Naira Biliyan uku a shekara. A kowace awa guda Dan wasan zai samu sama da Miliyan guda na Naira.

Dama dai kun ji cewa Idan komai ya yiwu Kungiyar Barcelona za ta saida Tauraron Dan wasan ta Neymar zuwa Kungiyar PSG na Faransa kan kudin da zai girgiza Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dalilin tsadar kaya a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel