Gawar marigayiya ɗiyar Sule Lamido ta iso Najeriya (Hotuna)
- Gawar yarinyar Sule Lamido, Hadiza Sule Lamido ta iso Najeriya
- Hadiza ta rasu ne a wani asibitin kasar India a ranar 29 ga watann Yuli
Da yammacin ranar Laraba 2 ga watan Agusta ne gawar yarinyar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido tai so filin sauka da tashin jirage na garin Dutse, da misalin karfe 6:27.
Wakilin jaridar Rariya ya ruwaito an hangi keyar manyan mukarraban tsohon gwamna Alhaji Sule Lamido a yayin tarbar gawar, wadanda suka hada da Alhaji Umaru, Malam Isah Duniya, Nasiru Roni, Aminu Ringim, Salisu Mamuda, Aminu Jahun, Rabiu Taura, Muhammad Habib Barded a ire irensu.
KU KARANTA: Jami’an Yansanda na neman wani ‘Malami’ wur-jan-jan sanadin abin daya aikata ma wata gawat (Karanta)
Legit.ng ta ruwaito Hadiza Sule Lamido mai shekaru 38 ta rasu ne bayan tayi jinya a wani asibiti dake kasar Indiya a ranar 29 ga watan Yulin data gabata.
Sa’annan ta rasu ta bar mijinta, yaya uku da iyayenta. Tun bayan rasuwarta ne tsohon gwamnan keta samun gaisuwar ta’aziyya tare da jajantawa daga jama’a ciki da wajen kasar nan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Dalilin dayasa farashin kayan abinci ke tashi:
Asali: Legit.ng