Kaji abun da za'a yi wa gidan tarihin Sukur da Boko Haram ta Kona a jihar Adamawa?
1 - tsawon mintuna
Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake kula da ababen tarihi da wurare watau NCMM a takaice ta bayyana cewa ta soma shiri-shiren don gyara gidan nan mai dadadden tarihi na garin Sukur a jihar Adamawa da kungiyar Boko Haram ta lalata.
Alhaji Yusuf Usman wanda yake zaman shugaban hukumar shine ya bayar da tabbacin hakan a garin Abuja da yake fira da yan jarida a jiya litinin.
Legit.ng ta samu labarin cewa Alhaji Yusuf Usman din ya kuma kara da cewa gyaran da hukumar tasu zata yi zai hada da na jihar Osun dake a garin Osogbo.
Ya kuma mika godiyarsa ga hukumar UNESCO da ta yi alkawarin tallafa wa gwamantin Najeriya da gyare- gyaren gidajen tarihin kasar.
Asali: Legit.ng