Shin wanene Gamji Ahmadu Bello Sardauna

Shin wanene Gamji Ahmadu Bello Sardauna

- An haifi Gamji Ahmadu Bello a 12 ga Watan Yuni 1909 a Garin Rabbah na Jihar Sokoto

- Mahaifin sa ya rasu yana shekara 6 a duniya zama kuma duk 'Yan uwan sa sun rasu

- Sunan Mahaifiyar Ahmadu Bello Mariyamu kuma Jikan Shehu Danfodio ne shi

Shin wanene Gamji Ahmadu Bello Sardauna
Gamji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto

1. Ya fara karatun addini wajen Mallam Garba Limamin kauyen su na Rabbah kuma ya fi kowa kokari a ajin su.

2. Sardauna ya shiga Teacher's Training College Katsina (Watau Barewa College)

3. A shekarar 1931 ga zama Malamin Makarantar Middle ga Sokoto.

4. Daga nan Sardauna ya zama Lawalin Unguwar su yana matashi

5. Ya nemi kujerar kakan sa ta Sarkin Musulmi bai samu ba inda Abubakar na III yayi nasara.

6. Ahmadu yana cikin manyan wannan Gwamnati amma daga baya aka samu matsala.

7. An daure Sardauna a gidan yari bisa laifin cin kudin haraji lokacin yana kamsila.

8. A shekarar 1944 bayan ya fito ya fara aiki a Gwamnati

9. A kuma shekarar 1949 ya tafi Majalisar dokokin Arewa

10. Sardauna ya dage wajen ganin mata sun yi ilmi.

KU KARANTA: Karatu na sa a gaba Inji 'Yar wasa

Shin wanene Gamji Ahmadu Bello Sardauna
Ahmadu Bello Sardauna da Tafawa-Balewa

11. A 1954 ya zama Firimiyar Arewa na farko. Shekara mai zuwa kuma ya tafi aikin Hajji

12. Ahmadu Bello bai damu da tara dukiyar Jama'a ba sai dai yi wa kasa aiki.

13. Maimakon ya zama Shugaban kasa sai Sardauna ya zabi Abubakar Tafawa Balewa ya tsaya a Arewa.

14. A 1959, Sarauniyar Elizabeth II ta ba shi Sandar girmar KBE don haka ake ce masa Sir.

15. A Oktoban shekarar 1962, ya kafa Jami'ar da ake kira Ahmadu Bello University ta Zaria ban da wasu kamfanoni a Arewa.

16. A farkon shekarar 1966 aka kashe Sardauna a gidan sa bayan dama ya ji kishin-kishin.

17. Sardauna ya mutu bai bar wani kudi ba a Duniya.

18. An kashe gwarzon ne tare da matar sa Hafsatu.

19. Wanda ya rena ne ya kashe sa a cikin gidan sa

20. Gamji yayi bakin kokarin sa wajen gina kasar Arewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An rage shekarun takara a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng