Jihar Kebbi ta fi ko ina zaman lafiya a Najeriya – Rochas Okorocha

Jihar Kebbi ta fi ko ina zaman lafiya a Najeriya – Rochas Okorocha

- Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yay aba ma jihar Kebbi saboda irin rawar da take takawa

- Okorocha ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da ba gwamnatin gwamna Bagudu goyon baya domin suji dadi moriyar damokradiya

- Ya kuma yi godiya ga sarkin Gwandu da masarautarsa kan gudunmuwarsu ga ci gaban jihar da ma kasar

Shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Rochas Okorocha ya bayyana jihar Kebbi a matsayin jiha mafi zaman lafiya a tarihin Najeriya,” NAN ta ruwaito.

Okorocha ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata 1 ga watan Agusta a Birnin Kebbi lokacin da ya jagoranci mambobin kungiyar domin kai ziyarar ban girma ga sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashir.

Ya kuma yaba ma gwamna Abubakar Bagudu da mutanen jihar da suka habbaka noman shinkafa da alkama.

Ya nuna yarda kan cewa Kebbi ta daukaka sunan Najeriya a cikin tutar kasashe a duniya ta fannin shinkafa.

Shugaban gwamnonin na APC ya yaba ma gwamna Bagudu kan kokarinsa na dawo da tattalin arzikin kasar ta hanyar noma.

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa a jihar Gombe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23

Ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da ba gwamnatin gwamna Bagudu goyon baya domin suji dadi moriyar damokradiya.

Ya kuma yi godiya ga sarkin Gwandu da masarautarsa kan gudunmuwarsu ga ci gaban jihar da ma kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel