Kunji labarin wanda ya yi dalilin aure sama da 1000
An samu wani mutum a kwaryar jihar Kano da ya yi sanadiyar hada aure fiye da dubu kuma ya yi fice wajen wannan abu da ya zamto aikin yi a gareshi
Wani mutum mai suna Malam Shua'aibu wanda a ka fi sani da Mai Dalilin Aure ya haddasa aure tsakanin maza da mata fiye da dubu a birnin Kano.
Malam Shu'aibu wanda tsohon ma'aikacin tsaro ne a jami'ar Bayero da ke Kano ya bayyana yadda ya fara wannan harka ta hada aure tun yana aiki a jami'ar ta Bayero a shekarar 1998.
Yace a lokacin da yake aikin tsaro ne ya lura da mata da maza da su ke shige da fice cikin jami'ar a motocinsu wanda hakan ya sanya ya fara kiran su ya na tambayar alakar da ke tsakaninsu inda a karshe ya ga babu mafita sai ya ga akwai bukatuwar taimakawa wajen hada aure tsakanin mata da mazan.
Tun a wannan lokaci abubuwa suka fara habaka ta yadda a yanzu Malam Shu'aibu ya yi fice wajen wannan harka don har suna aka baiwa layin gidan shi na layin Mai Dalilin Aure.
KU KARANTA: An dakatar da wasu mata 3 maniyyata aikin hajji a jihar KwaraAn dakatar da wasu mata 3 maniyyata aikin hajji a jihar Kwara
Malam Shu'aibu wanda mazaunin unguwar Liman ne cikin babbar unguwar Dorayi ta karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano, ya bayyana cewa yana jn dadin wannan aiki na shi don saboda a yanzu wadanda su ke zuwa neman mazaje ko matan aure ba iya ka cin kasar nan su ka tsaya ba don har daga wasu kashe irin su Nijar, Kamaru da Sudan.
Mai Dalilin aure ya bayyana matsalar da yake fuskanta wajen wadanda ya yi mu su aiki da cewa wasu ba sa sallamar shi idan ya mu su aiki wanda abin sallamar ta shi shine turmin atamfa guda daya tak ba ragi ba kari.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng