'Yan Kudu maso yammacin Najeriya ke jawo mana matsala a fannin gyara a Kasa tun 1953' - Tanko Yakasai

'Yan Kudu maso yammacin Najeriya ke jawo mana matsala a fannin gyara a Kasa tun 1953' - Tanko Yakasai

- Alh. Tanko Yakasai dai tsohon dan siyasa ne tun jam'hiruya ta biyu

- Siyasar zamaninsu cike take da kabilanci da bangaranci

- Ya yi tsokaci kan yadda siyasa take a yau

Tanko Yakasai, 91, yana daya daga cikin dattijan ’yan siyasa da suke da masaniya a siyasar Najeriya tun kafin kasar ta samu ’yanci daga hannun turawa. Yayi aiki da Shugaba Shehu Shagari inda yake mai bada shawara ta musamman da kuma mai tattaunawa da ’yan majalisa da yawun shugaban a Jamhuriyya ta Biyu. Bayan haka kuma yana cikin wadanda suka kafa kungiyar nan dake hada kan shuwagabannin arewa, wato Arewa Consultative Forum, ACF.

A wannan tattaunawa da aka yi da shi, Yakasai yayi magana a kan yadda kudu-maso-yamma na Najeriya tayi amfani da sauyin da aka yi a lokacin turawa don ta cimma burinta na mulke kasar. Sannan kuma yayi magana a kan cewa bai ji dadi ba da yadda masu kula da rashin lafiyar Shugaba Buhari suke tafiyar da al’amarin.

'Yan Kudu maso yammacin Najeriya ke jawo mana matsala a fannin gyara a Kasa tun 1953 - Tanko Yakasai
'Yan Kudu maso yammacin Najeriya ke jawo mana matsala a fannin gyara a Kasa tun 1953 - Tanko Yakasai

Shin Arewa tana tsoron sabon sauyin tsarin mulki?

Da faurko dai, maganar neman sauyi a Najeriya ta fara dauko asali ne daga musu son su mamaye kasar tun 1953. Kungiyar Action (asalin ta daga kudu-maso-yammacin Najeriya) ce ta kai maganar majalisar wakilai ta hannun marigayi Cif Anthony Enahoro, cewa turawa ya kamata su bawa Najeriya ’yanci a shekarar 1956. A lokacin ban san mutum nawa ne suka gama jami’a ba a yammacin Najeriya amma tabbas sun kai dubunnai, amma a lokacin Arewa mutum daya take dashi wanda ya gama jami’a, Dr R A Dikko, wanda turawa suka dauki nauyin karatun sa.

Saboda wannan tagayyara wakilan Arewa suka ce bai kamata a bada ’yanci ba sai sa’ar da hakan ya canja. Tunanin da wakilan suka yi shine in aka sake aka bawa Najeriya ’yanci a lokacin da Kungiyar Action ta so, to su zasu mamaye kasar su mulke ta su kadai.

Tun daga wancan lokaci har zuwa yau maganar sauyi tsarin kasa magana daya ce take ta canja fuska da salo. An yi maganar ana so a kirkiri sababbin jihohi a kasa; Kungiyar Action ta auna taga cewa haka zai sa ta iya samun ’yan jihohi daga Arewa da Gabashin Najeriya, ta zo hada da nata yawan don ta samu Fira-Minista daga cikinta. A lokacin irin mulkin turawan Birtaniya muke yi.

A kidayar 1963, Arewacin Najeriya na da jama’a kaso 55 cikin 100 na mutanen da ke Najeriya, gaba daya kudancin Najeriya kuma suna da kaso 45. A maimakon a bawa Arewa kujerar wakilai a majalisa yadda yayi dai-dai da yawan al’ummar ta, sai aka yi raba dai-dai da ’yan Kudu. A sakamakon hakane har yasa suka ingizo da maganar fidda sababbin jihohin.

Jami’iyyar NCNC ta zo tayi karfi a yammacin Najeriya sosai har ta kai da sai da ta shiga yankin Kungiyar Action a yankin kudu-maso-yamma. Da Kungiyar Action taga haka, sai ta maida hankalin ta kan Arewa don ta samin magoya baya daga nan. Amma da aka yi zaben 1959, jami’iyyar Arewa ta Northern People Congress ta lashe kusan gaba daya kujerun da aka baiwa Arewa a majalisa.

A 1961/62, shuwagabannin Kungiyar Action ta tabbatar ba zata iya kamo Arewa ba in dai har za ayi zabe na gaskiya, kuma ba zata mulki Najeriya ba. Wannan shine yasa suka yi makarkashiyar juyin mulki a 1962, inda aka kama shuwagabanni da dama. Bayan wannan juyin mulkin shine Najeriya ta dau salon mulkin turawan Amurka inda ba fira-minista sai dai shugaban kasa. Duk da haka Kungiyar Action ta zo ta kara shan kashi a sabon mulkin, wacce jam’iyyar NPN ta ci.

Da suka rasa yadda za suyi, sai suka hada kai da Social Democratic Party, SDP, inda suka goya wa MKO Abiola baya. Da aka zo kuma aka kansile zaben Abiola, sai suka canja suna suka koma NADECO. Bayan mutuwar Abacha da Abiola kuma sai suka koma PRONACO; haka sukayi ta yi. Da PRONACO ma ta ki karbuwa sai suka sake canjawa zuwa Sovereign National Conference, don su batar da cewa daga kudu-maso-yamma suke.

Abin da sukayi niyyar yi a SNC shine suna so su hada kai da wasu daga cikin ’yan Arewa da Kudu. Duk da haka basu sami yadda suke so ba; sai suka ingizo keyar ’yan jihohin da ake hakar mai a cikin su dan kar a samu zaman lafiya a kasar.

A maganar samin sauyi, har yanzu ba wanda ya kawo cikakken bayanin yadda ya kamata a sauya tsarin mulkin Najeriya. Shin in aka yi, yaya kasar zata koma, kuma mai zai faru dani, da kai, da kowa na kasar?

In amsa tambayar ka ta farko, shugabannin Arewa basa shakkar a ce za ayi sauyin tsarin Najeriya saboda sun san dole da su a cikin wadanda zasu sa baki. In za ayi sauyin tsari sai an bi dokokin kundin tsarin mulki. Saboda haka kafin a sami matsaya sai kaso biyu cikin uku na majalisar kasa da na jihohi sun goyi bayan maganar. Ina sha maka alwashin hakan bazai yiwu ba sai Arewa ta goyi bayan maganar saboda ita kadai dana da jihohi 13. Kuma kafin ’yan Arewa su goyi bayan maganar, sai sun san yadda Najeriya zata kasance bayan sabon tsarin. Saboda haka duk wanda yake da yadda tsarin zai kasance, ya kawo shi gaba a gani. Baka taba jin wani dan Arewa ya fito yace baya son a canja tsarin Najeriya ba. Ba ayi mana dai-dai ba ake cewa muna tsoron samun sabon sauyi a kasa.

Daga yadda ka yi bayani, jihohi basa jin dadin wannan yanayi da ake ciki; kuma…

Tsaya. Ba dai-dai bane a dau jihohin Najeriya 36 gaba daya a kan feji daya. Muna alakanta kan mu da Amurka bayan ba haka bane.

Jihohi 13 ne na Amurka sukayi ta ta tata-burza a kan samun ’yanci daga turawan Birtaniya masu mulkin mallaka. Sai suka hada kai suka kwaci ’yanci, sannan suka hada gwamnati guda daya. Daga baya sai wasu jihohi suka yi ta mubayi’a har sai da yau jihohin Amurka sun kai 50.

Jihohi ne suka hada Amurka, a maimakon Najeriya wadda kasar ce ta hada jihohi. A saboda haka ne jihohin Najeria basu da ta cewa a kan tsarin cibiyar mulkin kasar.

Najeriya ta samu asali ne daga yakuna uku wadanda turawa suka hade su a 1914: Yankin Kudu, Lagos (inda turawa suka sauka), da kuma Yankin Arewa. Sai bayan an jima ne da yin hakane sosai sannan aka shigo da yankin Gabas a wajajen 1921.

Ba jihohi bane suka hada Najeriya, Najeriya ce ta hada jihohi da kuma tsarin mulkin ta. Saboda haka in Najeriya ta yanke hukunci kuma ka gani cewa mafi yawancin shuwagabanni sun goyi baya, sai aka sami wata makarkashiya daga wani yankin, to ingizo su akeyi kawai don saboda zabon-kasa. Sannan kuma masu ingizo su suna da kafofin yada labarai yadda za ayi ta yada maganar.

A iyakacin sani na, har yau babu wani shugaba da aka zaba, na jiha ko na kasa, da yake goyon bayan maganar ya kamata Najeriya ta samu sabon tsari. Wadanda suke wannan magana suna yi ne kawai, don mafi yawancin ’yan kasar basa goyon bayan maganar.

Kana magana da yawun Arewa ne gaba daya? Don IBB da Atiku suna ta maganar ya kamata a sake sabon tsari…

IBB ya mulki Najeriya har tsawon shekara 8 a mulkin soja, Atiku shima 8 a matsayin mataimakin shugaban kasa a mulkin farar hula. Da suka fara maganar goyon bayan sabon tsari na ji dadi sosai don su suke da masaniya a kan yadda tsarin yanzu yake tafiya. Amma da na saurare su, sai naji duk dalilan su iri daya ne. Na fahimci cewa mulkin soja daban yake da farar hula saboda haka nayi wa IBB uzuri. Amma Atiku, dan siyasa kamar sa, ya kamata ya san kundin tsarin mulkin kasa ciki-da-bai.

Yace za’a iya sauya gaba daya tsarin kasar a cikin wata shida. Yace bajet din da akayi na ma’aikatun Ilimi da na ’yan Kwadago ya kamata ya koma hannun jihohi; kuma za’a iya yin haka a cikin wata shida.

Shin ya manta majalisar dattijai da wakilai na kasa su sukayi amince da wannan bajet a din bisa kundin tsarin mulki, kuma sai kawai a debi kudin a mika wa jihohi ba tare da an bi kundin tsarin mulkin ba? Ko da kuwa wakafi kadai za’a canja a cikin kundin tsarin mulki sai an bi dokokin da aka gindaya don kare tashin hankali a gaba.

Ya kamata Atiku ya kara bincike tukunna ya gani shin ya za ayi hakan ta harkar dai-dai.

Menene cece-kucen da akeyi game da harkar rashin lafiyar Shugaba Buhari?

Ban ji dadi ba akan yadda masu tafiyar da kula da rashin lafiyar Shugaba Buhari ba suke tafiyar da al’amarin. Kamata yayi su fito fili su fadi kome yake damun shi don kowa ya sani.

A lokacin da aka kwantar da shugaban Amurka Ronald Reagan, masu kula da al’amarin sun fito fili sun fadi mai ke damun sa, wanda haka yasa duk kasar aka yi ta yi masa fatan Allah ya sauwake. Ya kamata muma muyi koyi da su a nan don kowa ya sani. Kin fadar a kaikaice yana gayawa masu son su sa hannun jari a Najeriya su dunkule hannayen su saboda tsoron ko me ka iya faruwa. Rashin fadar ba taimakon kasar yake yi ba.

KU DUBA: Karyar banza ce, ba wanda yaje ya ga Buhari

Harkar tsaro fa?

Yawanci fadace-fadacen da ake ta cewa ana yi a Najeriya a cikin jaridu ne kawai da kafofin yada labarai don a tashi hankalin al’umma. Ba dai-dai bane a ce Najeriya na cikin tashin hankali bayan in ka duba Kano, Sokkwato, Jos, Kaduna, Lagos, Benin, Akure, Enugu da sauran jihohi da yawa ba abin da ke wanzuwa sai zaman lafiya tsakanin mazaunan garin da baki.

Amma, abin da kawai nake jiyewa shine, shuwagabanni sun musgunawa ’yan kasar har tsawon lokaci mai yawa wanda sai an yi duba a kan haka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: labaranhausa@corp.legit.ng

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng