Abinda ka shuka, shi zaka girba: Mutumin daya fyaɗe ýar shekara 3 ya gamu da hukuncin kisa (Hotuna)

Abinda ka shuka, shi zaka girba: Mutumin daya fyaɗe ýar shekara 3 ya gamu da hukuncin kisa (Hotuna)

- Kotu ta yanke ma wani mutumi da yayi ma yar shekara 3 fyade har ta mutu

- An zartar ma wannan mugun mutum hukuncin kisa bainar jama'a

Wani mutumin kasar Yemen da kotu ta tabbatar masa da hukuncin kisa bayan kama shi da aka yi da laifin hallaka wata karamar yarinyar mai shekaru 3 ta hanyar fyade, ya gamu da gabansa.

A ranar Litinin 31 ga watan Yuli ne aka zartar ma mutumin mai suna Muhammad Al-Maghrabi hukuncin kisan ta hanyar dirka masa harsasai har guda biyar a baya, kuma a gaban daruruwan jama’an garin suna kallo.

KU KARANTA: Samame a gidan gwamna Kashim Shettima a Abuja, EFCC tayi ƙarin haske

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito an tsaurara tsaro a yankin maghrib, garin wannan mutumi don gudun kai harin ramuwa ga jama’an garin daga yan uwan yarinyar.

Abinda ka shuka, shi zaka girba: Mutumin daya fyaɗe ýar shekara 3 ya gamu da hukuncin kisa (Hotuna)
Jami'an tsaro tare da mutumin

Shima mahaifin yarinyar, Yahaya Al-Matari ya bayyana ma manema labaru bayan an kashe mutumin da yayi ma yar tasa fyade, cewa ji yake kamar yau aka haife shi saboda bakin cikinsa ya kau.

Abinda ka shuka, shi zaka girba: Mutumin daya fyaɗe ýar shekara 3 ya gamu da hukuncin kisa (Hotuna)
Mutumin gab da za'a kashe shi

“Ji nake kamar yau na shigo duniya, na samu sauki a raina sosai” kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli barnar da Boko Haram tayi:

Asali: Legit.ng

Online view pixel