Biyafara: Kadan ya rage mutane na su harbe dan kungiyan IPOB da ya tare wa Obiano hanya - Garba Umar

Biyafara: Kadan ya rage mutane na su harbe dan kungiyan IPOB da ya tare wa Obiano hanya - Garba Umar

- Jami'an tsaro ba za su kyale masu karya doka ba

- Kada kayi abun da zaki yi da na sani

- Da kyar jami'an tsaro suka shigar da gwamnan cikin motar sa

Kwamishinan yan sandar jihar Anambra, Garba Umar yace kadan ya rage mutanen sa su bude wa yan kungiyan IPOB wuta a lokacin da suke tare wa gwamnan jihar Anambra Willie Obiano hanya.

Masu fafutikar neman biyafara sun tunkaro Obiano a lokacin da yake cikin St.Joseph’s Catholic church, dake Ekwulobia Jihar Anambra.

Yan sanda sun yi iya kokarin wajen ganin cewa basu harbe kowa ba.

Byafara:Kadan ya rage mutane na su harbe dan kungiyan IPOB da ya tare wa Obiano hanya-Garba Umar
Byafara:Kadan ya rage mutane na su harbe dan kungiyan IPOB da ya tare wa Obiano hanya-Garba Umar

Wani a wajen ya ce, da kyar jami’an tsaro suka samu nasaran shigar da gwamnan cikin motar sa.

KU KARANTA: Jigawa: PDP ta mika ta'aziyya ga tsohon gwamnan jihar Jigawa kan rasuwar ‘yarsa

Kwamishinan yan sadar jihar Garba Umar yace hukuma ba za ta kyale masu karya doka ba musamman irin wannan barazana da aka yiwa gwamnan jihar Anambara a lokacin da yake wajen ibada.

“Mai yasa za suyi zanga-zanga a coci, ai coci wurin bautan Allah ne amma da alaman suna da niyyan jikkata gwamnan ne."

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, yace zaben da za ayi a jihar Imo, ba zai yiwu ba.

Amma Obiano ya gargade shi da cewa kada ya kuskara ya aikata abun da zai yi danasani.

Mako biyu da yagabata wasu matasa da ake zargin su da zaman yan kungiyan IPOB, suka hana ruwa guda a wani taro da dan takaran jam’iyyar APGA Godwin Ezeemo ya halarta a Odoekpe, dake karamar hukuman Ogbaru.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Ga masu shawara

Ga Masu korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng