Yaki da ta’adanci: Sojojin sama ta karo dakaru na musamman da kuma kayan aiki zuwa Arewa maso Gabas

Yaki da ta’adanci: Sojojin sama ta karo dakaru na musamman da kuma kayan aiki zuwa Arewa maso Gabas

- Dakarun sojin Naf zasu yi aiki tare da sojojin kasa

-NAF ta gabatar da kyamara na mussaman da zai taimaka wajen gano yan kuna bakin wake

-An dauki matakai na mussaman dan wargasa kungiyan Boko-haram

Sojojin sama na Najeriya(NAF) ta gabatar da Karin matakan da ta dauka wajen magance matsalolin ta'adanci a Arewa maso gabas. Matakan su hada da Karin sojojin NAF special forces dan karfafa tsaro, zasu yi aikin hadin gwiwa da sojojin kasa tare da sojojoin sama da suke a wajen tuntuni.

Bugu da kari, NAF ta gabatar da kyamara na mussaman da zai taimaka wajen gano yan kuna bakin wake kafin su kai hari a ko ina. Wannan ya biyo bayan har-haren da yan kunar bakin suka yawaita kai wa a cikin kwananan a Maiduguri.

Yaki da ta’adanci: Sojojin sama ta karo dakaru na musamman da kuma kayan aiki zuwa Arewa maso Gabas
Yaki da ta’adanci: Sojojin sama ta karo dakaru na musamman da kuma kayan aiki zuwa Arewa maso Gabas

Kyamaran yana da na’uran da zai iya gane mutumin da ke zuwa daga nesa kuma yana iya gane yanyin jikin mutu. kyamarori, wanda aka daura shi a saman jirgin NAF, yana iya gani komai a cikin hayaki, hazo, da ruwan sama.

KU KARANTA:https://hausa.legit.ng/1117566-dalilin-ziyara-ta-gidan-buhari-da-ke-landan-reno-omokri.html

NAF a cikin kwanakin nan ta kara dauka matakai dan rage karfin Boko-haram a Arewa maso Gabas. Ta mayar da hankali wajen gano inda mayakan boko-haram suke zama, da da kuma baiwa mutanen yankin agaji dan samun yardar su. NAF ta na mika godiyar ta zuwa ga yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke samu wajen su dan ganin cewa sun magance matsalar ta’adanci a Arewa maso gabas

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel