Kimiyya: Shin tsakanin kwakwalwa da zuciya? Wacce masu rai ke amfani da ita wajen tunani?

Kimiyya: Shin tsakanin kwakwalwa da zuciya? Wacce masu rai ke amfani da ita wajen tunani?

A zamunna na da, ba'a ma san da me dan-adam ke amfani wajen tunani ba. A lokuta da dama a tarihi, an zaci da zuciya ake tunani, sai da zamani ya zo, ilimi ya ratsa, sannan aka san menene amfanin kwakwalwa. Wannan har yanzu wasu jama'ar Hausawa basu iso fahimtar hakan ba.

A fahimta ta ilimi, kwakwalwa ita ce ke tafiyar da gangar jiki, babu wani bangare na jikin dan-adam da yake aika sako ga ko ina ayi wani aiki sai kwakwalwa. Ita ko zuciya, bata da wani aiki banda aiki daya, buga jini ga sauran sassan jiki.

Kimiyya: Shin tsakanin kwakwalwa da zuciya? Wacce masu rai ke amfani da ita wajen tunani?
Kimiyya: Shin tsakanin kwakwalwa da zuciya? Wacce masu rai ke amfani da ita wajen tunani?

A zamanin da, lokacin ba wani ilimi sai shaci fadi, da chanki-chanka, kowa ya hakura a kan cewa zuciya ce ke aiwatar da komai, wanda sanin hakan bisa kuskure, ya gina yaruka, da al'adu har ma da addinai a kan hakan.

A misali, a addinin Misirawa na da can, na Fir'aunoni, idan mutum ya mutu, wanda su a al'adarsu, suna so ne su adana gangar jiki, saboda wai yayi sabuwar rayuwa a karkashin kasa, watau 'underworld' kamar dai kace lahira, sukan cire kayan ciki na gawa su adana a kwalabe, amma suna barin zuciya, domin a tunaninsu, a nan rai yake.

DUBA WANNAN: Sanata Kwankwaso ya shilla kasar Masar ceto, ko wa yaje cetowa?

Haka ma Girkawa, sukan ce ai kwakwalwa wata aba ce da ke sako majina zuwa hanci, domin sanyaya jiki idan zafi yazo, sun zaci kwakwalwa ke narkewa ta tsiyayo ta hanci a matsayin majina.

Larabawa, Yahudawa da ma Turawa, sun kuskure kan batun zuciya, inda suka gina addinansu bisa rashin sanin cewa ita zuciya, wadda take cikin kirazan mutane, ita ke tafiyar da tunani, kuma ita ke bada damar magana, idan ma anyi in-iina, ita zuciya wai ita ke sarke harshe. Basu da masaniya ashe kwakwalwa ce ke aikin, zuciya bata da alaka da magana ko harshe.

ZAKU SO WANNAN: Labarin Hitila da yakin Duniya na biyu

A al'adance ma dai, an yi babban kuskure, inda ake dangana harkar soyayya da zuciya, a duk wani yanayi na soyayya, wanda ake kira 'emotions', wato bege, wanda kwakwalwa ke tafiyarwa, zaka samu ana danganta shi da cewa zuciya ke aikin.

An tafka irin wadannan kura-kurai a lokuta da dama, inda har zaka ji wake-wake da ke cewa kina zuciya ta, ko zuciya na kuna, wannan duk kuskure ne, komai yana kwakwalwa. Babu komai a zuciya banda jini.

KARANTA: Albashin Ma'aikata a sauran kasashen duniya, dubi wadanda suka yi mana nisa

A cikin dubunnan shekaru da aka gina harsuna kan wannan kuskure, ya kasa zama jiki a tsakanin jama'a, inda aka kasa gyara yaren cewa zuciya ke aiki, duk da wasu al'ummun sun gane. Shekaru dai basu fi dari biyu ba da aka san meye ainahin aikin kwakwalwa.

A yanzu dai jama'ar arewacin Najeriya da yawa basu ma san da wannan ilimi ba, koda yake sun san hakan a aji, basu iya wuce makaranta da wannan ilimi, saboda al'adu da addinai kullum suna dora so a kan batun wai da zuciya ake tunani.

Idan an kula, za'a gane cewa, mai cutar zuciya, mai hawan jini, ko ma wanda aka saka wa zuciyar roba saboda kasawar tasa, basu rasa hankalinsu, saboda hankali bashi da alaka da zuciya, haka zalika, wanda ke da tabin hankali, baka samunsa yana rike zuciya yana kukan tana ciwo, saboda matsalarsa a lantarkin da kwakwalwa ke harbawa ce.

Faduwar gaba kuma, mai ras dinnan, wadda tsoro ke haifarwa, kwakwalwa ce ke gaya wa zuciya ta bugo jini maza-maza, domin da shi take aiki, kwakwalwar kuma ta gaya wa idanu cewa su bude sosai, ta kuma gayawa tsoka, a zo a gudu, saboda a tsira, wannan haka yake a dukkan mai rai banda tsirrai.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng