Matar da aka ceto daga hannun Boko Haram ta koma bayan taji labarin mijinta yayi sabuwar mata
- Wata mata da aka ceto daga hannun Boko Haram ta koma ga mijinta dan Boko Haram
- Matar ta koma ne bayan ta samu labarin mijin nata yayi sabon aure
Kishi ya damu wata mata da aka ceto daga hannun mayakan Boko Haram a watan Feburairu bayan ta samu labarin tsohon mijin nata dan Boko Haram yayi sabuwar amaryar, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Sakamakon hakan ya sanya wannan mata sake komawa ga tsohon mijin nata duk da irin hatsarin da hakan ke tattare da shi.
KU KARANTA: Cutar yoyon fitsaro: Ministan Lafiya yayi ma marasa lafiya tiyata a asibiti da kansa (Hoto)
Ita da wannan mata mai suna Aisha Yarima ta tsere ne daga gaban iyayenta tare da dna yaron data haifa da tsohon mijin nata dan Boko Haram, kamar yadda Binyu Yarima, kanwar Aisha ta bayyana.
Duk kokarin da aka yi na dawo da Aisha gida yaci tura, saboda bata daukan kiran ake yi mata a wayanta, daga bisani ma kashe wayar tayi.
Kimanin shekaru hudu da suka gabata ne kungiyar Boko Haram ta sace Aisha, amma Sojojin Najeriya sun ceto ta tare da wasu mutane su 70 a watan Feburairun data gabata, bayan nan aka kais u wani sansani don basu kulawa na musamman.
A wani bayani da Aisha tayi bayan an ceto su, tace a matsayinta na matar kwamandan Boko Haram, tana samun alfarma da dama da suka hada da bayi da samun isashshen abinci.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Yadda ake sana'ar mayar da Bola kayan amfani, kalla:
Asali: Legit.ng