An bada belin Saminu Turaki

An bada belin Saminu Turaki

Rahotanni sun kawo cewa wata babbar kotun Tarayya dake babban birnin tarayya Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki.

An saki tsohon gwamnan ne a yammacin ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli bayan kama shi da hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kama shi.

A farkon wannan watan ne hukumar ta EFCC ta damke shi a babban birnin tarayya Abuja.

Kafin bada belin nasa, kotu ta shimfida masa sharuda na kawo mutane biyu wanda ko wanne a cikin su zai jinginar da N250,000,000 a gaban ta.

An bada belin Saminu Turaki
An bada belin Saminu Turaki Hoto: Premium Times Hausa

KU KARANTA KUMA: Labari Yanzu-Yanzu: Shugaban Pakistan ya rattaba hannu kuma ya sauka daga mulki a yau, me yayi zafi?

Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba tare da rakiyar iyalai da ‘yan uwan tsohon gwamnan ne ya karbi belinsa a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng