Biyafara: Wata Matashiya ‘yar Najeriya ta samu takadar kudin Biyafara a akwatin kakanta (Hotuna)
- Wata matashiya ta ce ta gano wasu takadar kudaden Biyafara a cikin wani akwatin kakanta
- Matashiya ta wallafa kudin ne a shafinta ta Facebook, yayin da ta ce tana alfari da kudin
- Nmesoma ta ce yanzu bakin alkalami ta bushe a kan kafa yankin Biyafara
Wata matashiya ‘yar Najeriya kuma memba na kungiyar 'yan asalin kafa yankin Biyafara (IPOB) ta samu wasu kofi na takadar kudin mutanen yankin Biyafara a cikin wani akwatin kakanta.
Matashiyar wanda aka gano a matsayin Nmesoma James, ta wallafa hotuna wasu takadar kudin ne a shafinta na Facebook yayin da ta ce ta samu kudadden ne daga cikin wasu kayyakin kakanta.
Legit.ng ta tattaro cewa, Nmesoma wanda ta kira kanta a matsayin 'Ada Biyafara', ta nuna kudin Biyafara ga magoya bayanta yayin da kuma ta ke gaskata cewa ta na alfahari da yankin Biyafara.
KU KARANTA: 'Ka tsare Kanu, domin ya saba ka'idar belin sa', Matasan Arewa suka fada ma Osibanjo
Kamar yadda Nmesoma James ta rubuta:
" Shaka babu za a kafa yankin Biyafara. Babu ruwan mu da maganganun mutane. Yanzu haka na gano wannan tsabar kudin Biyafara a cikin wata akwatin kakanmu,duk kudin mutanen Biyafara ne zalla”.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng