Gwajin Kanjamau da Sinadarin Jini ya zama wajibi ga masu shirin aure a Bauchi
Gwamnatin Jihar Bauchi ta zartar da dokar Gwajin Jini ga masu shirin aure a Jihar.
Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa dokar tilastawa masu shirin aure da su gudanar da gwajin sinadarin Jini da ciwon Kanjamau kafin aure.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a taron da masu ruwa da tsaki suka gudanar na kungiyar kula da masu dauke da ciwon Kanjamau, Kuturta da Zazzabin cizon Sauro ta Jihar Buachi.
Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta kafa dokar da sunan ‘Dokar wajibcin gwajin Sinadarin Jini, Ciwon Kanjamau da daina nuna bambanci ga masu dauke da Cutar 2017.’
Dokar ta hada da wajibcin gwajin Sinadarin Jini da ciwon Kanjamau kafin aure don kare masu dauke da cutar daga tsangwama, da nuna bambanci.
KU KARANTA KUMA: An samu Attajirin da ya bige Bill Gates a Kudi
Dokar zata kare mutunci da hakkin masu shirin aure, da mutane masu dauke da ciwon Kanjamau ko ciwon Sikila.
Dokar ta sanya sharadin cewar dole Iyaye su kai ‘Ya’yansu zuwa gwajin Jini, da bayyana sakamakon kafin su aurar da su.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng