Kalli wadanda Yansanda suka kama masu garkuwa da mutane a Kaduna

Kalli wadanda Yansanda suka kama masu garkuwa da mutane a Kaduna

- Rundunonin tsaro a jihar Kaduna na cigaba da samun nasarar cafke masu garkuwa da mutane

- Rundunar Operation yaki ta kama masu garkuwa da mutane su biyu

Rundunar tsaro ta jihar Kaduna, Operation Yaki ta samu nasarar kama wanu jiga jigan miyagu dake sace sacen mutane a jihar Kaduna da kewaye, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Mutanen da aka kama su hada da Habu Lawal Na’asabe da Anas Danlami inkiya Baushe, dukkaninsu matasa masu matsakaicin shekaru, inji majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Dakarun Soji sun ƙwato muggan makamai daga mayaƙan Boko Haram (Hotuna)

Jami’an rundunar tsaro ta Operation yakin dai sun dana tarkunansu akan wadannan miyagun mutane, inda suka cafke su a kauyen Kargo Dam dake yankin Jaji, cikin karamar hukumar Igabi.

Kalli wadanda Yansanda suka kama masu garkuwa da mutane a Kaduna
Masu garkuwa da mutane a Kaduna

Idan za'a tuna, a cikin wannan satin ne ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya kawo ziyarar gani da ido wuraren da ake yawan samun sace sacen mutane, inda ya zazzagaya tare da gwamnan jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli gidan kasurgumin mai yin garkuwa da mutane:

Asali: Legit.ng

Online view pixel