Yadda Bezos ya doke Bill Gates a matsayin mai kudin Duniya

Yadda Bezos ya doke Bill Gates a matsayin mai kudin Duniya

– Yanzu haka Jeff Bezos ya fi kowa kudi a Duniya

– Har ta kai wannan Attajiri yayi gaba da su Bill Gates

– Jeff Bezos ya samu kudin sa ne ta Kamfani Amazon

Kowa ya san cewa Attajiri Bill Gates shi ya fi kowa kudi a Duniya na dogon lokaci tun ba yau ba. Kwatsam sai ga wani hamshakin mai kudi ya sha gaban shi.

Yadda Bezos ya doke Bill Gates a matsayin mai kudin Duniya
Masu kudin Duniya Jeff Bezos da Bill Gates

Tun shekaru 24 da suka wuce kenan kowace shekara Bill Gates yana cikin manyan Attajiran Duniya. Mista Bill Gates shi yake da fitaccen Kamfanin nan na Microsoft. Sai dai yanzu Mista Bezos yayi gaba ya bar Gates.

KU KARANTA: An doke Bill Gates a mai kudin Duniya

Yadda Bezos ya doke Bill Gates a matsayin mai kudin Duniya
Hoton Bill Gates mai Kamfanin nan na Microsoft

Bezos ne wanda ya mallaki Kamfanin Amazon da ake saida kayan litattafai da sauran su. Bill Gates dai ya dage wajen kawar da cutar zazzabin masassara a Afrika kowace shekara. Ko bana dai Gates ya kashe Dala Biliyan 3.1 wajen wannan harka.

Ba don irin wannan kokari ba dai babu yadda za ayi Bezos ya doke Bill Gates don ko a haka da Dala miliyan 500 ne rak Bezos ya zama na daya a Duniya. Haka kwanakin baya mai kudin kasar Sifen Amancia Ortega ya doke Bill Gates na dan lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka so ka kara dawowa Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel