EFCC na tuhumar hadimin Sarkin Musulmi kan badaƙalar naira miliyan 700
Hukumar yaki da almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta fara gudanar da bincike na musamman akan asusun ajiyar fadar Sarkin Musulmi dake karkashin kulawar shugaban ma’aikatan fadar, Kabiru Tafida.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Tafida, EFCC ta kama Sarkin Fadan masarautan Sakkwato, sai dai daga bisani an sallamo shi a ranar Talata 25 ga watan Yuli.
KU KARANTA: Tafiya Landan: Yadda tattaunawar mu da Buhari ta kasance – Abdul Aziz Yari
Majiyar Legit.ng ta ruwaito sashin bincike na hukumar EFCC ne suka gano musayar kudaden da aka yi da suka kai naira miliyan 700, da aka aika su sai biyu daga asusun gwamnatin jihar Sakkwato.
Dayake hannun EFCC, Sarkin Fadan Sakkwato ya bayyana cewa an turo da kudaden ne don a siyan ma Sarkin gida a babban birnin tarayya Abuja.
“Mun fara zargin lauje cikin nadi ne tun daga lokacin da muka ga an aika kudaden cikin asusun wani mutum, ban a masarauta ba. Sa’annan akwai wasu korafe korafe dangane da kudaden da ake turawa asusun Kabiru Tafida.” Inji jami’in EFCC.
sai dai Kaakakin gwamnatin jihar Sakkwato Imam Imam ya musanta wannan zargi, inda yace wadannan kudade na cikin kasafin kudin bana, kuma an bi doka da tsari wajen fitar da kudaden, haka zalika majalisar zartarwa jihar Sakkwato ta gamsu da fitar da wadannan kudade.
Haka zalika ofishin Sakataren gwamnatin jihar da ma’aikatan gine gine da sifiyo ne suka zagaya don binciko gidan da za’a siyan ma Sarkin don zama idan ya isa garin Abuja.
Daga karshe Imam Imam ya bayyana takardun dake nuna sahihancin fitar da kudaden.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Matasan Najeriya sun yi zanga zanga: Kalla:
Asali: Legit.ng