A hanyar Kano zuwa Daura aka binne sihirin da akayiwa Buhari
Rahotanni sun kawo cewa wani shahararren shehin malami da aka mabata da suna Aliyu Jibia ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa lallai yana sane da cewa sihiri akayiwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.
A cewar Arewablog.com, malamin ya bayyana cewa a jumhuriyyar Nijar aka je aka shiryo sihirin da akayiwa shugaban kasar kuma sannan aka binne shirin ne a hanyar Kano zuwa Daura.
Aliyu Jibia ya wallafa wannan ne a shafinsa inda ya kara da cewa wannan shine amsar da yaba shafin Mikiya.
Ya bayyana cewa shine mutun na farko wajen Sanar da duniya wannan tun a shekarar 2016 amma ba kowa ya basar da zancen.
A cewar malamin: “Rubutu da na wallafa akan 'Bamagujen Dan Boko' duk nuni ne akan na kewaye da Buhari, kuma sihirin a jumhuriyyar Nijar aka shiryo shi, amma a hanyar Kano zuwa Daura aka binne shi.
KU KARANTA KUMA: Osinbajo zai rantsar da sababbin ministoci gobe
“Na yi iya bakin kokari na don aikawa shugaban kasa da gudunmawa da zaá warware sihirin ta hanyoyin makusantansa, amma bai je gareshi ba. A karshe, na gaji, kuma na hakura”.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#
Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng